Dokar ta ɓaci: Majalisar wakilai ta kaddamar da kwamitin wucin gadi mai mutum 21 da za su sa ido kan gwamnatin jihar Rivers

Reps new 750x430

Majalisar wakilai ta kaddamar da kwamitin wucin gadi mai mambobi 21 da za su sa ido kan gwamnatin rikon kwarya a jihar Rivers a yanayin da take ciki na dokar ta-baci.

A zaman majalisar na ranar Talata, Kakakin majalisar, Tajudeen Abbas, ya ce kaddamar da kwamitin ya yi daidai da sashe na 11 (4) na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima).

Yayin da yake jaddada kudirin majalisar dokokin kasar na tabbatar da shugabanci na gaskiya a Najeriya, Abbas ya bukaci kwamitin da ya kasance ba tare da nuna son kai ba.

A cewarsa, kwamitin zai sa ido kan yadda ake aiwatar da umarni da manufofin gwamnatin tarayya a Rivers, tare da tabbatar da cewa gwamnatin riko ta bi doka.

Abbas ya bukaci ‘yan kwamitin da su gudanar da aikinsu ba tare da nuna son kai ko sanya ido kan kowane bangare na gwamnatin rikon kwarya ba kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Karanta: Alkali ya yi murabus daga mukaminsa domin nuna rashin amincewa da nadin da aka yiwa Ibas na shugabancin jihar Rivers

Yayin da yake yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan matakin da ya dauka a jihar Rivers, kamar yadda sashe na 305 na kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, ya ce hakan na nuni ne da nagartar jagoranci.

Kakakin majalisar ya bukaci shugaban mulkin jihar Rear Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya da ya kasance mai nuna gaskiya wajen gudanar da ayyukansa, yana mai cewa gwamnatinsa ta wucin gadi ce.

Da yake mayar da martani, Shugaban kwamitin, Julius Ihonvbere, ya gode wa shugaban majalisar da ya dauki wannan mataki.

Ihonvbere, farfesa kuma shugaban masu rinjaye na majalisar, ya yi alkawarin ba za su yi kasa a gwiwa ba ga majalisun kasa da ma ‘yan Najeriya baki daya wajen sauke nauyin da aka dora musu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mambobin kwamitin sun hada da: Ali Isa, mataimakin shugaban, Isiaka Ibrahim, Idris Wase, Aliyu Betara, Sada Soli, James Faleke, Igariwey Enwo, Shehu Rijau da Wole Oke.

Sauran sun hada da: Akarachi Amadi, Patrick Umoh, James Barka, Alex Egbona, Isa Anka, Amos Daniel, Erhiatake Ibori-Suenu, Onuh Onyeche, Fatima Talba, Chris Nkwonta da bibake Enenimiete. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here