Darasin Lissafi ba zai zama dole ba ga ɗaliban ilimin fasaha masu neman shiga jami’a – gwamnatin tarayya

Maruf 750x430

Gwamnatin tarayya ta amince da sabon tsarin gyaran sharuddan karɓar ɗalibai a dukkan manyan makarantu a ƙasar nan domin sauƙaƙa samun damar shiga jami’a da sauran cibiyoyin ilimi.

Sanarwar hakan ta fito ne a wata takarda da daraktar yada labarai da hulɗa da jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Folasade Boriowo, ta sanyawa hannu a ranar Talata.

Ta bayyana cewa wannan sabon tsarin gyara ya samo asali ne daga ministan ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, a matsayin wani ɓangare na aiwatar da shirin “Sabon Fata” domin faɗaɗa ilimi mai haɗa kowa da kowa a matsayin ginshiƙin cigaban ƙasa.

A ƙarƙashin sabon tsarin, gwamnatin tarayya ta ce tana son ta cire manyan shingayen da ke hana ɗalibai samun gurbin karatu, amma tana tabbatar da cewa aji na ilimi ya ci gaba da daidaituwa da ƙa’idodi.

Wannan tsarin zai shafi jami’o’i, kwalejojin fasaha (polytechnic), kwalejojin ilimi (college of education), da cibiyoyin bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire (Innovation Enterprise Academies – IEAs) a fadin ƙasar.

Dakta Alausa ya bayyana cewa wannan gyaran ya zama dole ne bayan dogon lokaci da ɗalibai da dama suka kasa samun gurbin karatu duk da cancantar su.

Ya ce sama da ɗalibai miliyan biyu ke rubuta jarabawar shiga jami’a (UTME) a kowace shekara, amma kimanin ɗalibai 700,000 ne kawai ake karɓa.

Ya ce wannan rashin daidaito ba saboda rashin basira ba ne, amma saboda tsoffin ƙa’idojin da suka yi tsauri.

Sabon tsarin, a cewarsa, zai ƙara damar karɓar ɗalibai daga 250,000 zuwa 300,000 a kowace shekara, don tabbatar da cewa ba a bar matasa masu iya aiki a baya ba saboda tsohon tsarin karɓa.

A cewar sanarwar, ga jami’o’i, sabuwar ƙa’idar ta tanadi cewa dole ɗalibi ya samu aƙalla darussa biyar da ya ci da ƙwarewa a cikin jarrabawa guda ɗaya ko biyu, ciki har da Turanci, yayin da Lissafi zai ci gaba da zama dole ne kawai ga fannoni na kimiyya, fasaha, da zamantakewa.

Ga kwalejojin fasaha (ND), ana buƙatar darussa huɗu da ɗalibi ya ci da ƙwarewa, ciki har da Turanci ga marasa kimiyya, da Lissafi ga fannoni na kimiyya.

Haka kuma ga shirin HND, ana buƙatar darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi.

Ga kwalejojin ilimi (NCE), ɗalibai dole su samu aƙalla darussa huɗu, inda Turanci yake zama dole ga fannoni na fasaha da zamantakewa, yayin da Lissafi ya zama dole ga fannoni na kimiyya, sana’o’i da fasaha.

Ga shirin digirin ilimi (B.Ed), ana buƙatar darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi.

Cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire (IEAs) kuwa za su yi amfani da irin wannan tsarin da ake amfani da shi a kwalejojin fasaha.

Haka kuma an soke takardar “National Innovation Diploma (NID)” tare da maye gurbin ta da “National Diploma (ND)” domin tabbatar da daidaituwa da sahihancin takardun.

Hukumar kula da ilimin fasaha ta ƙasa (NBTE) ta samu umarni da ta sake duba da tabbatar da sahihancin dukkan IEAs a faɗin ƙasar domin su daidaita da sabon tsarin.

Ministan ya ce, kowace cibiyar da ta kasa cika wannan sharadi za a cire mata lasisin aiki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here