Dan jaridar PRNigeria da aka sace ya shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe fiye da mako guda a hannun masu garkuwa

Salis Manaja 750x430

Dan jaridar kamfanin Image Merchants Promotion Limited (IMPR), masu wallafa PRNigeria da Economic Confidential, Salisu Muhammad Manaja, ya samu ‘yanci bayan shafe fiye da mako guda a hannun masu garkuwa da mutane.

Shugaban sashen binciken gaskiyar labarai na IMPR, Muhammad Dahiru Lawal, ya tabbatar da sakin Manaja a ranar Alhamis, inda ya ce an sako shi ne da yammacin Laraba, kuma yanzu haka yana tare da iyalinsa lafiya.

Ya kara da cewa Manaja ba ya tare da wani rauni mai tsanani, amma za a kai shi asibiti don duba lafiyarsa.

Lawal ya bayyana godiya ga duk wanda ya taimaka, ya yi addu’a ko ya nuna goyon baya ga iyalan Manaja yayin tsarewarsa, yana cewa irin wannan tallafi ya ba su kwarin gwiwa a lokacin da ake cikin tashin hankali.

Majiyoyi daga cikin iyalan Manaja sun shaida cewa an biya kudin fansa kafin a sako shi.

A cewar majiyar, masu garkuwar sun fara neman Naira miliyan 20, amma daga baya aka cimma yarjejeniya da kudi kasa da hakan bayan tattaunawa.

Idan za a iya tunawa an sace Manaja ne a garin Ogugu da ke karamar hukumar Olamaboro ta jihar Kogi, lokacin da yake kan hanyarsa daga Abakaliki a jihar Ebonyi zuwa Ilorin a jihar Kwara domin halartar shirin horar da matasan ‘yan jarida na shekara-shekara da IMPR ke gudanarwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here