Kotun daukaka kara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yanke ranar 10 ga watan Janairu wanda ya tabbatar da matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na soke dokar majalisar masarautun ta shekarar 2019, har sai an yanke hukuncin daukaka kara a kotun koli.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a Kano ta yi watsi da umarnin da Mai Shari’a Abubakar Liman na babbar kotun tarayya da ke Kano ya bayar a ranar 20 ga watan Yuni, inda ta soke matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka bisa dokar masarautar Kano ta 2024, ciki har da nadin Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16.
Kotun daukaka kara ta Kano da ta zauna a Abuja, ta ce hukuncin da ya soke matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka a karkashin dokar majalisar masarautu ta 2024 mai shari’a Liman ne ya bayar da shi ba tare da wani hurumi ba.
A don haka kotun ta ce bata gamsu da hukuncin ba, wanda hakan ya sa gwamnatin jihar Kano ta daukaka kara zuwa kotun koli inda daga bisani ta shigar da kara a kotun daukaka kara inda ta bukaci kotun da ta dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an yanke hukuncin daukaka kara a kotun koli.
Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a da wasu alkalai uku karkashin jagorancin Mai shari’a Okon Abang a kararraki biyu masu lamba CA/KN/27M/2025 da CA/KN/28M/2025, wanda Alhaji Aminu Babba Dan’agundi ya shigar.
Karin karatu: Jami’an tsaro sun kewayw gidan Sarkin Kano Sanusi tare da hana shige da fice
An shigar da karar ne a kan gwamnatin jihar Kano, da kakakin majalisar dokokin kasar, da babban sufeton ‘yan sanda, da hukumar tsaron farin kaya ta kasa da jami’an tsaron farin kaya, da sauran hukumomin tsaro.
Aminu Baba Dan’agundi (Sarkin Dawaki Babba) ne ya shigar da karar a ranar 6 ga Fabrairu, 2025, inda ya nemi umarnin hana wadanda ake kara aiwatar da hukuncin kotun daukaka kara a yayin da ake ci gaba da daukaka kara a kotun koli.
Dalilin da ya sa aka shigar da karar shi ne tun da farko wanda ya shigar da karar ya shigar da ita ne a Kano don kare masa hakkinsa, sai dai kotun da ke shari’ar ba ta da hurumin saurare, don haka akwai bukatar a hana wadanda ake kara aiwatar da hukuncin.
Bugu da kari, mai karar ya ce, dokar da majalisar dokokin jihar ta kafa ta 2024, wadda majalisar dokokin jihar ta amince da ita, kuma gwamnan ya amince da ita, ta hanyar doka ne ya sanya aka rusa sabbin masarautun da aka kafa tare da mayar da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16.
A cikin hukuncin da aka yanke, kwamitin mutane uku na alkalai karkashin jagorancin Abang, sun bayyana cewa bukatar ta dace da hukumcin kotun domin samun adalci domin ya cika dukkan sharuddan doka da ake bukata don samun agajin da ake nema.
Kotun ta hana wadanda ake kara aiwatar da hukuncin da aka yanke ranar 10 ga watan Janairu wanda ya soke rusa masarautun da gwamnatin jihar Kano ta yi.
Har ila yau, ta ba da umarni, tare da ci gaba da kasancewa har sai Kotun Koli ta yanke hukunci na karshe.