Ministan tsaron Najeriya, janar mai ritaya Christopher Musa, ya bayyana cewa rashin tsaro na ci gaba da ƙamari a ƙasar ne sakamakon yadda wasu mutane da al’ummomi ke ɓoye ’yan bindiga, ’yan ta’adda da sauran masu aikata laifuka daga hannun hukumomin tsaro.
Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja a yayin bikin bayar da lambar yabo karo na 7 ta OurNigeria News Awards, inda ya jaddada cewa Najeriya na fuskantar wani sabon salo na rikici na zamani da ba za a iya shawo kansa da ƙarfin soji kaɗai ba, sai da cikakken haɗin kai daga jama’a.
Ministan ya bayyana cewa irin wannan rikici na zamani na faruwa ne a cikin al’umma, inda makiya ke rayuwa a tsakiyar jama’a suna ɓoye kansu a matsayin talakawa, lamarin da ke sanya tattara bayanan sirri da kai rahoto cikin gaggawa ya zama muhimmin ginshiƙi wajen kawo ƙarshen ta’addanci.
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su rika kai rahoton duk wani nau’in aikata laifi kamar garkuwa da mutane, ’yan bindiga, ta’addanci da tayar da ƙayar baya, tare da tabbatar da cewa hukumomin tsaro za su ɗauki mataki cikin gaggawa da ƙwarin gwiwa.
Christopher Musa ya nuna cewa halin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar na ci gaba da inganta a hankali, sakamakon ayyukan soji da ake ci gaba da yi, ƙarfafa tattara bayanan sirri da kuma goyon bayan jama’a.
Tun da fari, sarkin masarautar Doma, Alhaji Ahmadu Onawu, ya bayyana cewa OurNigeria ba kafar yaɗa labarai kaɗai ba ce, illa saƙon kishin ƙasa, fata da farfaɗowar ƙasa, yana mai cewa Najeriya tana da wadatattun mutane masu basira da albarkatun ƙasa amma gazawar amfani da su yadda ya kamata ne babban ƙalubalen da ke gabanta.
A nasa jawabin, mai wallafa mujallar OurNigeria News, Dakta Sani Abubakar, ya bayyana cewa ainihin saƙon bikin bayar da lambar yabo shi ne gaskiya da sahihanci, inda ya ce, ana karrama nagarta ba tare da alaƙa da kuɗi ko siyasa ba, tare da ambaton misalin gudunmawar da wani ɗan agaji daga Jihar Gombe ya bayar ga ƙungiyoyin Kiristoci da Musulmi a matsayin alamar juriya, haɗin kai da zaman lafiya.
NAN













































