Hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta bayyana cewa ta zabi wani kamfani da yi hidima ga maniyyata aikin hajjin shekarar 2025 a sakamakon wasu kalubalen da ake fuskanta na gudanar da aikin da Mashariq al Dhahabia.
Sanarwar da shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar NAHCON, Muhammad Ahmad Musa ya fitar, ta bayyana cewa Mashariq al Dhahabia, wanda a baya shi zai yi hidima ga daukacin alhazan Najeriya a kasa mai tsarki wanda tun farko ya sanya hannu kan kwangilar, sai dai ya fuskanci kalubalen da ka iya hana dukkan mahajjata gudanar da aikin.
Idan dai za a iya tunawa Mashariq al Dhahabia ya yi barazanar kai karar hukumar NAHCON saboda karya kwangilar saboda hukumar ta ba wani kamfani kwangilar daukar nauyin alhazan Najeriya a ranar Masha’ir, kwanaki biyar da mahajjata ke kwana a tanti a Muna, Arafah da Muzdhalifah a birnin Makkah.
Karin karatu: Hajj 2025: Kashim Shettima ya umurci NAHCON ta warware matsalolin da ka iya zama barazana
Kamfanin dai ya yi ikirarin cewa hakan ya saba wa yarjejeniyar cewa shi ne kamfani daya tilo da zai yiwa alhazan Najeriya hidima a tsawon wannan lokaci don haka ya baiwa NAHCON kwanaki 20 domin tattaunawa.
Sai dai Musa a cikin sanarwar ya ce hukumar na tattaunawa da kamfanin na kasar Saudiyya Mashariq al Dhahabia game da zargin karya kwangilar.
Ya ce tun da aka kafa hukumar NAHCON ta cika dukkan alkawurran da ta dauka na kwangila, tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana da kuma a ranar 17 ga watan Janairun 2025, a ziyarar da ta kai gabanin Hajjin bana bayan bikin baje kolin Hajji, NAHCON da Mashariq al Dhahabia suka kulla yarjejeniya don samar da kulawa a Masha’ir ga mahajjatan Najeriya.
Daily Trust