Dalilanmu na bada fifiko a yaƙi da miyagun ƙwayoyi- Ribadu

WhatsApp Image 2025 06 04 at 15.25.34 750x430

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin tarayya na ba da fifiko wajen yaki da miyagun kwayoyi sakamakon tasirin da ta ke da shi ga tsaron kasa da kuma walwalar al’umma.

Haka kuma ya alakanta amfani da haramtattun abubuwa musamman a tsakanin matasa abinda ke ta’azzara karuwar rashin tsaro, yana mai cewa yawancin ‘yan ta’adda na yawan cin zarafial’umma.

A cewarsa, hakan na kara rura wutar aikata laifuka da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar kasa.

Ribadu, ya kuma ce, gwamnati ta jajirce wajen tallafa wa ayyukan da hukumomi ke ci gaba da yi na kai hare-hare kan haramtattun magunguna da na jabu.

Ya kuma jaddada cewa, manufarsu ita ce kawar da kasar daga abubuwa masu hatsarin da ke cutar da al’umma.

Da yake jawabi yayin wani taro tsakanin hukumomin a ofishinsa da ke Abuja, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa shirin ya wuce bin doka da oda kadai har da farfado da zaman lafiya.

Ya bayyana shi a matsayin tsoma baki a fannin kiwon lafiyar jama’a na tsawon lokaci tare da babban tasiri ga tsaron kasa.

Ribadu ya kuma gargadi masu sayar da haramtattun magunguna da kayan maye da cewa ba za su ci gaba da kasuwanci kamar yadda aka saba ba.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da mara baya ga yakin da wannan matsala har sai an samu ci gaba mai ma’ana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here