Daliban BUK sun karrama mawallafin jaridar Solacebase Abdullateef Jos kan bin ƙa’idojin aikin jarida da taimakon al’umma

IMG 9186 750x430

Ƙungiyar Daliban masarautar Ilorin (IESU) da ke karatu a Jami’ar Bayero Kano ta karrama Malam Abdullateef Abubakar Jos, babban Edita kuma mawallafin kafar labarai ta internet Solacebase, bisa goyon baya mai ɗorewa da yake bai wa ƙungiyar, da gudummawar sa ga bin ka’idojin aikin jarida da kuma rahotannin jinƙan al’umma.

Bikin miƙa lambar yabon ya gudana ne a wajen wani taron bita da ƙungiyar ta shirya mai taken “Ba wai abin da ake yayi ba kawai: Jarida mai ma’ana”, wanda aka gudanar a sashin koyar da aikin jarida na zamani ka jami’ar ranar asabar.

A cikin jawabin maraba, shugaban sashen koyar da aikin jarida na zamani Farfesa Nura Ibrahim, ya yaba da jagorancin ƙungiyar bisa shirya taron da ya bayyana a matsayin mai cike da fa’ida.

Ya ce daliban Kwara a Jami’ar BUK sun kasance masu ƙarfi a jami’ar tun daga farko.

Ya ce taron ya zo ne a lokacin da matasa da dama ke maida hankali kan abubuwan da ke yawo a kafafen sada zumunta ba tare da yin tunani kan tasirin da hakan zai iya yi ga mutuncinsu ba.

Shi ma, malami a sashen nazarin bayanai da kafofin yaɗa labarai, Dakta Saminu Umar, ya yi bayani kan amfani da na’urorin zamani aikin da yadda ake ba da labari ta kafar zamani.

A jawabin sa na musamman, Malam Abdullateef Jos ya lissafo muhimmam matakai da ’yan jarida da masu ƙirƙirar shirye-shirye suka kamata su bi, inda ya jaddada muhimmancin rikon amana, bin manufa, da ƙwarewar aiki.

Ya bukace su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa, rubutu cikin kwarewa, fifita gaskiya akan hanzari, da kula da gaskiyar abin da suke wallafawa.

Ya kuma jaddada muhimmancin samar da ingantaccen shiri mai ma’ana, wayar da kan jama’a, haskaka batutuwan jinƙai ga al’umma, da bai wa marasa galihu, ciki har da mata da mutanen da ke fama da nakasa, damar isar da muradunsu.

Ya ce kafafen jarida su rika samar da shiri da zai inganta rayuwar al’umma da tattalin arziki tare da nuna tausayi ga masu sauraro.

A bangaren kayan aiki da dabaru, ya bukaci yin amfani da kayan tantance gaskiya, dogaro da bincike da bayanai, kiyaye ka’idojin zamani, haɗa muryoyin al’umma, da yin amfani da basirar tantance bayanai da abubuwan da ke yawo.

Jos, ya bukaci ’yan jarida su ɗaga darajarsu sama, su mayar da hankali kan samar da jarida mai ƙarfafa dimokuraɗiyya, inganta al’umma, da kawo canji mai kyau.

Yayin taron, shugaban ƙungiyar, Kwamared Ibrahim Salau Olarewaju, ya ce wannan horo ya zama dole saboda yadda wasu matasa ke yawan wallafa abubuwan da suka saba da tarbiyya a intanet don kawai su samu masu kallo ba tare da yin tunani kan sakamakon hakan ba.

Ya kawo misalin wasu shafuka a Instagram da TikTok da ke tattauna batutuwan batsa don neman mabiya.

Ya shawarci matasa su wallafa abubuwan da ya kamata, su kuma yi amfani da kafafensu wajen ilmantar da jama’a.

Yayin mika lambar girmamawa ga Malam Abdullateef Jos, shugaban ƙungiyar ya ce halayensa da tsarin aikinsa abin koyi ne, har ma ya ce shi uba ne a gare su wanda koyaushe yake sauraron su idan suna buƙatar taimako.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here