Sama da daliban kur’ani 300 daga jahohin Arewa shida ne suka hallara a jihar Bauchi domin gudanar da gasar karatun kur’ani na gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi karo na biyu.
Jihohin sun hada da Bauchi, Gombe, Kano, Katsina, Niger, da Kaduna.
Bikin bude taron wanda aka gudanar a ranar Lahadi a Bauchi, ya nuna yadda aka fara gudanar da shirin na tsawon mako guda, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 4 ga watan Mayu zuwa 10 ga watan Mayu.
Da yake jawabi a wajen taron, Sakataren Ilimi na Gidauniyar Malam Abdullahi Ismail, ya ce an gudanar da gasar ne da nufin inganta karatun kur’ani mai tsarki kamar yadda aka saukar ga Annabi Muhammad (S.A.W).
Ya ce taron ya kuma kara karfafa kwarjini da jajircewar daliban Alkur’ani.
“Gidauniyar ta kaddamar da wannan gasa ta Musabaqa na karatun Alkur’ani na shekara-shekara, wadda ta hada da bangarorin Fiqhu, Tauhid, da Sira, ga dalibai a fadin Najeriya da makwaftan kasashe.
“An tsara shi ne don zurfafa ilimin addinin Musulunci da kuma daukaka ilimin Kur’ani,” in ji Ismail.
Ya kara da cewa taron na shekara-shekara zai ci gaba da karfafa tushen ilimin addinin musulunci a fadin yankin.
Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Tijjani Dahiru, ya kwadaitar da dalibai da su dauki Alkur’ani a matsayin jagorar rayuwarsu.
Ya jaddada mahimmancin ci gaba da karatunsa da haddace shi don ci gaban ɗabi’a da tsarkn zuciya.
A nasa jawabin, Dakta Mujitapha Abdulkadir, ya yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su tallafa wa shirin ta hanyar kafa cibiyoyi na dindindin da za su karbi bakuncin mahalarta gasar da kuma bunkasa gasar. (NAN)