Dakta Dahir M. Hashim ya bayyana ƙwarin guiwa a ci gaban da ya dace da yanayi

515042589 3370060753141128 9083126809369747989 n 750x430

Kwamishinan Muhalli da Sauyin yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahir M. Hashim, ya bayyana kwarin guiwar Najeriya na samun ci gaban da ya dace da yanayi ta hanyar haɗa kai da sabbin hanyoyin samar da kuɗaɗe.

Dakta Hashim, wanda ya kasance cikin waɗanda suka jagorancin tattaunawa ranar Laraba a wajen taron raba ababen more rayuwa a Najeriya na shekarar 2025 da aka gudanar a ɗakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja, ya bayyana gaggawar daukar matakan da suka dace wajen tinkarar kalubalen da ke tattare da matsalolin sauyin yanayi yayin da ake ƙoƙarin bunƙasa masana’antu da kuma birane.

SolaceBase ta ruwaito cewa, taron mai taken “Kashe Kuɗi don Ci gaba mai dorewa, “ya ​​tattaro fitattun shugabanni da masana da masu kirkire-kirkire daga sassa da dama na nahiyar Afirka da ma wajenta.

Dakta Hashim, ya halarci taron zuba jari da hadin gwiwa na gwamnati da masu zaman kansu, inda shi da sauran masu ruwa da tsaki suka tattauna hanyoyin da za a iya yin amfani da su don hanzarta zuba jari a shirye-shiryen da za su iya jure matsalolin yanayi a sassa masu mahimmanci kamar makamashi da sufuri da ci gaban birane da kuma fannin noma.

Haka kuma, ya yaba wa ofishin mataimakin shugaban ƙasa da hukumar kula da sauyin yanayi ta ƙasa da sauran masu ruwa da tsaki kan shirya abin da ya bayyana a matsayin taron da ya dace da kuma tsare-tsare.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here