Tsohon dan takarar gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar PDP, Dr Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ya bayyana sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Ficewar Jandor zuwa APC na zuwa ne makonni biyu kacal bayan ya fice daga PDP.
Tsohon jigon PDP na Legas ya bayyana ficewar sa ne a wani taron manema labarai a ofishin yakin neman zaben sa da ke Ikeja ranar Litinin.
A kwanakin baya Jandor ya tattauna da shugaban kasa Bola Tinubu, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da wasu jiga-jigan siyasa bayan ficewar sa daga PDP.
Karanta: Yanzu-yanzu: Majalisar dokokin jihar Rivers ta zargi Fubara da mataimakiyarsa da rashin ɗa’a
Mai magana da yawun sa, Gbenga Ogunleye ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis din da ta gabata cewa ganawar da shugaban ya yi ne a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce, “Ina iya tabbatar da cewa Dr Abdul-Azeez Olajide Adediran Jandor ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Litinin (makon da ya gabata).
“Tun da farko ya gana da mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida, tsohon shugaban kasa, Gen. Abdusalami Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar SDP a zaben 2023, Prince Adewole Adebayo, da sauran fitattun shugabannin kasa. Yana daga cikin tuntubar da yake yi bayan ficewarsa daga jam’iyyar PDP.
“Sakataren jam’iyyar PDP na kasa da sauran shugabannin jam’iyyar su ma sun ziyarce shi a kwanan baya don neman a sake duba batun ficewa daga PDP.