Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori Sanata Basheer Mohammed Lado, Darakta Janar na Hukumar Hana Fataucin Mutane ta Kasa (NAPTIP).
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar.
Sanarwar ta ce shugaban ya amince da nadin Dr. Fatima Waziri-Azi a matsayin wanda zai maye gurbin Mohammed.
”Nadin ya biyo bayan shawarwarin da ministar kula da ayyukan jin kai da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouq ta yi, ” in ji sanarwar.
Ya ce Ministar ta bayyana “bukatar hukumar ta NAPTIP ta kara kaimi domin cimma muhimman nasara.”
A cewar sanarwar, Hajiya Sadiya ta ce Fatima Waziri-Azi tana da asali mai kyau” da gogewa kuma za ta yi amfani ingantacciyar hanyar da ta dace don ciyar da hukumar gaba.













































