Shirye-shiryen ƙungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super Eagles, don fafatawa da ƙasar Gabon a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya ta 2026 ya gamu da cikas bayan ‘yan wasan da jami’an tawagar suka kaurace wa atisaye a Rabat saboda rashin biyan hakkokinsu da alawus.
Rahotanni sun nuna cewa duka ‘yan wasa da jami’an tawagar sun ƙi fita atisaye a ranar Talata saboda matsalar jinkirin biyan kuɗaɗen da suke bi daga hukumar kwallon ƙafa ta ƙasa.
Wannan yajin aiki ya faru kwanaki biyu kacal kafin Super Eagles su kece raini da Gabon a Rabat, a wasan farko na matakin kusa da na ƙarshe na gasar zakarun nahiyar Afirka don neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya. Da
Kafin wannan rikici, tawagar Najeriya ta nuna kwarin gwiwa bayan zuwan ɗan wasa Victor Osimhen wanda ya haɗu da sauran ‘yan wasa 22 a sansani, tare da mayar da hankali kan dabarun wasa da atisaye.
Sai dai yanzu rashin biyan hakkokin ya jefa tawagar cikin rudani yayin da ake ganin rashin daidaiton kuɗi daga hukumar kwallon ƙafa ta ƙasa ya jawo fushin ‘yan wasa.
Hukumar kwallon ƙafa ta Najeriya (NFF) ba ta fitar da wata sanarwa ba tukuna, amma ana sa ran tattaunawa ta ci gaba domin warware matsalar kafin a ci gaba da atisaye.
Idan an samu daidaito kafin lokaci, Super Eagles za su ci gaba da atisaye a gobe Laraba domin shirye-shiryen fafatawa da Gabon a wasan da ake ganin yana da matuƙar muhimmanci ga Najeriya.













































