Da ɗumi-ɗumi: PDP ta lashe dukkanin kananan hukumomi 30 a jihar Osun

PDP PDP 750x430

An bayyana jam’iyyar PDP a matsayin wadda ta lashe dukkan kujerun shugabanni da kansiloli a dukkanin kananan hukumomi 30 na jihar Osun.

Shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta ta jihar Osun (OSSIEC), Hashim Abioye, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Asabar.

Karanta: Za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Osun duk da shawarar Babban lauyan tarayya

Abioye ya bayyana cewa ’yan takarar jam’iyyar PDP sun samu nasarar lashe dukkan kujerun kansiloli a dukkanin mazabu 332 da ke jihar, da kuma zaben shugabannin kananan hukumomin jihar 30.

Gwamnatin jihar Osun dai ta ce zaben kananan hukumomin ta da aka yi a ranar Asabar ya samu kashi 60 cikin 100 na masu kada kuri’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here