Da ɗumi-ɗumi: Kotun ƙoli ta tabbatar da ɗaurin shekaru 6 ga John Yusuf tare da maido fiye da Naira biliyan 22

Yakubu Yesufu 678x381 1
Yakubu Yesufu 678x381 1

A yau Laraba ne kotun ƙoli ta tabbatar da zaman gidan yari na tsawon shekaru shida ga tsohon daraktan fansho na tarayya FDP, Mista John Yakubu Yusuf, tare da umartasa da ya mayar wa gwamnatin tarayya Naira Biliyan 22 da miliyan 900.

Solacebase ta ruwaito cewa maƙudan kudin da kotun ta umarci ya dawo da su ya kwashe su ne daga cikin asusun fansho na ƴan wanda aka shigar da sanda da ƙara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja cewa an karkatar da su.

Mai shari’a Tijjani Abubakar a hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara da tsohon Daraktan ya shigar, kotun ƙolin a yau ta tabbatar da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke a shekarar 2018 wadda ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru shida a gidan gyaran hali, baya ga maido da maƙudan kuɗaɗen.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here