Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam’iyyar PDP daga gudanar da babban taronta na kasa da aka shirya yi a birnin Ibadan na jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba.
Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke wannan hukunci bayan ya karɓi ƙarar wasu ‘ya’yan jam’iyyar uku da suka nuna rashin jin daɗinsu kan yadda ake tafiyar da shirin taron.
Kotun ta bayyana cewa jam’iyyar ta saba wa kundin tsarin mulkin ƙasa na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, da ƙa’idojin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, da kuma kundin tsarin mulkin jam’iyyar kanta wajen shirya taron.
Rahotanni sun nuna bayyana cewa jam’iyyar ta kasa gudanar da sahihin taron jihohi kafin ta fara shirin babban taron da nufin zaɓen shugabannin ƙasa na jam’iyyar.
Kotun ta umarci jam’iyyar da ta koma ta daidaita harkokinta, sannan ta aike da sanarwar kwanaki ashirin da ɗaya kamar yadda doka ta tanada kafin a ci gaba da shirin taron.
Masu shigar da ƙarar su ne shugaban jam’iyyar PDP a Imo, Austin Nwachukwu; shugaban jam’iyyar a Abia, Amah Abraham Nnanna; da sakataren jam’iyyar a yankin Kudu maso Kudu, Turnah Alabh George, inda suka nemi kotu ta dakatar da gudanar da taron gaba ɗaya.
Kotun ta yi watsi da ƙalubalen da jam’iyyar ta gabatar tana cewa batun cikin gida ne, inda ta tabbatar da cewa tana da ikon dakatar da taron har sai an cika dukkan sharuddan doka kafin gudanar da shi.












































