Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi wata ganawar sirri da wasu jiga-jigan jam’iyyar NNPP daga Kano.
Wadanda aka yi ganawar da su sun hada da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Sulaimaiman Abdurrahman Kawu sumaila da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano/Kibiya/Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Dala Hon. Ali Madaki da tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Danbatta Makoda Hon. Badamasi Ayuba.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban jam’iyyar APC na kasa kan harkokin sadarwa nAminu Dahiru, ya tabbatar da taron a wani sako da ya wallafa a kafafen sada zumunta a ranar Talata a Abuja.
Wannan na daga cikin a shirye-shiryansu na ficewa daga jam’iyyar NNPP dan komawa jam’iyyar APC.
Karanta: PDP za ta zama tarihi idan Atiku ya samu tikitin takarar shugaban kasa a 2027 – Bode George
Sanin kowa ne a kwanakin baya an jiyo wadannan jiga-jigan suna bayyana irin rashin adalcin da jagoran NNPP Kwankwasiyya Dr Rabi’u Kwankwasiyya ya ke musu.
Wannan dalili ya sa su ke kokarin ficewa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC.