Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) mai barin gado, Farfesa Mahmood Yakubu, ya mika ragamar shugabancin hukumar ga Misis May Agbamuche-Mbu, wadda za ta rike matsayin shugabarl ta riƙon ƙwarya.
An gudanar da bikin mika ragamar ne a ranar Talata yayin taron da yake gudana tsakanin Farfesa Yakubu da kwamishinonin zaɓe na jihohi (RECs) a cibiyar hukumar da ke Abuja.
Misis Agbamuche-Mbu, wadda ita ce tsohuwar kwamishina mafi dadewa a cikin hukumar, za ta kula da harkokin gudanarwa na INEC har sai an naɗa sabon shugaba.
Farfesa Yakubu ya bayyana cewa ya mika shugabancin hukumar a hukumance ga Misis Agbamuche-Mbu, tare da kira ga sauran kwamishinoni da daraktoci su ci gaba da bayar da goyon baya da haɗin kai kamar yadda suka yi masa.
Wannan sauyi ya zo ne a daidai lokacin da hukumar ke ci gaba da shirye-shiryen gudanar da wasu muhimman ayyukan zaɓe a faɗin ƙasar nan.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa Misis Agbamuche-Mbu, wadda ƙwararriya ce a fannin mulki da lauyanci, ta kasance a cikin kwamitin gudanarwa na INEC tun bayan nadinta, kuma ana sa ran za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da ake gudanarwa a cikin hukumar.













































