Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta ayyana yajin aikin gargadi na makonni biyu a faɗin ƙasar nan, domin bai wa gwamnati damar kammala tattaunawa da ƙungiyar kan batutuwan da suka jima suna jayayya a kai.
ASUU ta umarci dukkan mambobinta a sassan ƙasar da su dakatar da gudanar da duk wani aiki daga tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025.
Shugaban ƙungiyar, Dakta Chris Piwuna, ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar ƙungiyar ta ƙasa da ke jami’ar Abuja.
Ƙungiyar ta zargi gwamnati da rashin gaskiya wajen tattaunawa da ita, lamarin da ya janyo wannan sabon mataki.
A cewar shugaban ƙungiyar, babu wani abin da ya isa a yanzu da zai hana aiwatar da kudirin kwamitin zartarwa na ƙungiyar na shiga yajin aikin gargadi bayan ƙarewar wa’adin kwanaki goma sha huɗu da aka bayar tun ranar 28 ga watan Satumba, 2025.
Labari mai alaƙa: Ƙungiyar ASUU ta gana da shugabannin ɗalibai, tare da bayyana dalilin da ya sa take shirin yin yajin aiki
Wannan sabuwar takaddama tsakanin ƙungiyar malaman jami’o’i da gwamnatin tarayya ta sake kunno kai ne duk da ci gaba da tattaunawa da ake yi domin kauce wa sake shiga wani yajin aiki a jami’o’in ƙasar.
Ƙungiyar ASUU ta sha yin kira ga gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a baya, da suka haɗa da batun albashi, tallafin bincike, da inganta kayan aiki a jami’o’i.
Wannan yajin aiki, kamar yadda kungiyar ta bayyana, na nufin tunasar da gwamnati muhimmancin gaggauta ɗaukar mataki kafin halin da ake ciki ya sake yin muni.
Ana sa ran yajin aikin zai shafi ɗalibai da jami’o’i da dama a ƙasar, musamman ma waɗanda ke ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya, yayin da ake jiran matakin da gwamnati za ta ɗauka a cikin makonni biyu na wannan yajin aiki.













































