Cire tallafin mai: Gwamnatin Ebonyi ta ƙara wa ma’aikata naira dubu goma-goma a kan albashi

1689350043522
1689350043522

Gwamnatin jihar Ebonyi ta amince da karin albashin N10,000 ga ma’aikata domin rage radadin cire tallafin man fetur.

Gwamnatin ta kuma amince da daukar ma’aikata 1,454 a jihar.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar, Engr Jude Okpor ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a kan sakamakon taron majalisar zartarwar jihar, wanda gwamnan jihar Francis Nwifuru ya jagoranta a Abakaliki babban birnin jihar.

Okpor ya ce: “Mai girma gwamna ya amince da a kara Naira 10,000 a kan albashin kowane ma’aikaci a jihar domin rage radadin cire tallafin man fetur.

Ya kuma bayyana cewa gwamnan ya amince da daukar ma’aikata 1,454 a ma’aikatun jihar domin cike guraben da babu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here