Kungiyar tsofaffin ɗaliban Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta ajin 1991 ta shirya taron walimar ban girma don taya murnar abokan karatunsu biyu da suka samu mukamin manyan shugabannin jami’a.
Wadanda aka yi wa girmamawar sun hada da Farfesa Haruna Musa Dambatta, wanda ya zama Shugaban Jami’ar Bayero Kano na 12, da kuma Farfesa Yahaya Isah Bunkure (Makaman Rano), wanda shi ne shugaban farko na Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Zariya.
Taron ya gudana cikin nishadi, inda aka yi addu’o’i, gabatar da juna, da jawabin maraba daga shugaban kungiyar, Alhaji Ibrahim Adamu Shamakeri.
Daga bisani aka mika musu katunan taya murna na musamman domin nuna girmamawa da yabawa ga nasarorin da suka samu.

An kuma gudanar da kade-kade, ciye-ciyenabinci, da jawaban taya murna daga abokan aiki da baƙi, tare da martanin masu girma Farfesoshi guda biyu, waɗanda suka nuna jin daɗin girmamawar da aka yi musu tare da alƙawarin ci gaba da ba da gudummawa ga ilimi, al’umma da kuma zumuncin ajin BUK 1991.

Daga cikin manyan baki akwai mambobin kungiyar daga sassa daban-daban na ƙasar nan ciki har da jami’an gwamnati, hukumomin tsaro, masana harkar kasuwanci da kuma jami’o’i.

Shugaban Asibitin kashi na Dala, Dakta Nurudeen Isah, shi ma ya halarci taron.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban kungiyar, Alhaji Sanusi Garba Abdullahi, ya yaba da hadin kai da jajircewar mambobin wajen taya juna murnar samun nasarori.

Ya ce wannan girmamawa ga Farfesoshin biyu alama ce ta haɗin kai da raya zumunci na ajin.
Taron ya ƙare da addu’a, daukar hotunan ƙungiya da kuma sada zumunci da ya nuna ɗorewar ƙauna da haɗin kan mambobin ajin BUK na shekarar 1991.













































