Mai riƙon shugabancin jihar Rivers Vice Admiral Ibok-Ete Ibas, ya amince da nadin sabbin shugabanni da mambobin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar, da kuma shugabannin ƙananan hukumomi.
A cewar sanarwar, sabon shugaban RSIEC, Dr Micheal Ekpai Odey, zai yi aiki da mambobi shida da kuma farfesoshi hudu.
An bayyana nadin ne a wata sanarwa ta musamman da gwamnatin ta fitar ranar Laraba ta hannun Farfesa Ibibia Worika, sakataren gwamnatin jihar Rivers.
Sanarwar wacce aka aike wa manema labarai ta ce nadin ya fara aiki ne daga ranar Litinin 7 ga Afrilu, 2025.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne Ibas ya dakatar da shugabannin ma’aikatu da hukumomin jihar da suka hada da RSIEC, karkashin jagorancin Mai shari’a Adolphus Enebeli (mai ritaya).
Shugabannin kananan hukumomi 23 na jihar Rivers sun hada da:
Mr Okroiyobi Animiete – karamar hukumar Abua/Odual
2. Mr Goodluck M. Ihenacho – karamar hukumar Ahoada ta gabas
3. Mr Promise Jacob – karamar hukumar Ahoada ta yamma
4. Dr Tamunotonye Peters – karamar hukumar Akuku Toru
5. Surveyor Atajit Francis –karamar hukumar Andoni
6. Barrister Ibiapuve Charles – karamar hukumar Asari Toru
7. Mr Kingsley N. Banigo – Karamar Bonny
8. Dr Sokari Ibifuro Francis – karamar hukumar Degema
9. Dr Gloria Obo Dibiah – karamar hukumar Eleme
10. Barr Franklin P. Ajinwon – karamar hukumar Emohua
11. Dr Onyemachi S. Nwankwor – ƙaramar hukumar Etche
12. Prof. Gospel G. Kpee – Karamar hukumar Gokana
13. Mr Isaiah Christian Nobuawu – karamar hukumar Ikwerre
14. Dr Barinedum Nwibere – karamar hukumar Khana
15. Dr Clifford Ndu Walter – karamar hukumar Obio Akpor
16. Dr Chukwuma Aje – kananan hukumomin Ogba/Egbema/Ndoni
17. Eliel Owubokiri – ƙananan hukumomin Ogu/Bolo
18. Mr Thompson Isodiki – karamar hukumar Okrika
19. Manager Ikechi Wala – karamar hukumar Omuma
20. Mr Fred Apiafi – kananan hukumomin Opobo /Nkoro
21. Eletuuo Ihianacho – karamar hukumar Oyigbo
22. Dr Sam Kalagbor – karamar hukumar Port Harcourt
23. Mr Nuka O. S. Gbipah – ƙaramar hukumar Tai
Sai kuma wadanda ya nada a matsayin shugabanni da mambobin hukumar zaben jihar da suka haɗar da:
1. Dr Micheal Ekpai Odey – shugaba
2. Mr Lezaasi Lenee Torbira – Mamba
3. Prof Author Nwafor – Mamba
4. Prof Godfrey Woke Mbgudiogha – Mamba
5. Prof Joyce Akaninwor – Mamba
6. Dr Olive A. Bruce – Mamba
7. .Prof Chidi Halliday – Mamba
Hakan ya biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke, wanda ta bayyana zaben ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar a ranar 5 ga Oktoba, 2024, a matsayin mara inganci.
Matakin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan wata babbar kotun tarayya da ke Fatakwal ta shirya ranar 14 ga Afrilu, 2025, don sauraren karar da lauyan kare hakkin dan Adam, Courage Nsirimovu na cibiyar Pilex Center for Civic Education Initiative ya shigar.
Nsirimovu na neman dakatar da nadin shugabannin kananan hukumomi a jihar.
Mai shari’a Adamu Mohammed wanda ke jagorantar al’amarin bai bayar da umarnin hanawa karara ba, sai dai ya umurci da a sanar da Shugaban rikon Jihar Rivers da ya bayyana dalilin da ya sa ba a amince da bukatar dakatar da nadin ba.