Tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorochas, ya ce yana fatan a rayuwarsa ya fitar da yara miliyan daya daga kan titi kuma ya basu ilimi mai inganci kyauta.
Okorocha, wanda ya wakilci Imo ta yamma a majalisar dattijai, ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin da yake zantawa da wasu ‘yan jarida a wani bangare na bukin murnar cikarsa shekaru 59 a ranar Alhamis.
A cewarsa, abin da ya fi mayar da hankali a shekarunsa 59 shine inganta ilimi ga marasa galihu, wadanda ba su da damar samun ilimi.
Okorocha ya ce ba da kulawa ta ilimi ga yaran da suka samu tsaiko a duk fadin Afirka yana da mahimmanci a gare shi fiye da samun abin duniya.
“Ina so in kwashe yara miliyan daya daga kan titi in ba su ilimi mai inganci kyauta, wannan shine manufa ta.
“Da zarar na sami damar cimma hakan, yafi mahimmanci a gare ni fiye da zama shugaban Najeriya, sanata ko gwamna.
“Wannan yana da mahimmanci a gare ni fiye da samun gidaje a Afirka ta Kudu da Dubai,” in ji shi.
Sanatan, wanda shine ya kafa Gidauniyar “Rochas Foundation”, ya ce a yanzu yana da yara sama da dubu 25,000 da yake kula da su a makarantu daban -daban.
Gidauniyar Rochas wata ƙungiya ce mai zaman kanta, kua ba ta siyasa ba wacce aka kafa a shekarar 1998.
Tana da ƙuduri yiwa ɗan adam hidima da gina kyakkyawar makoma ga Afirka ta hanyar tabbatar da kowane mai ƙarancin gata ya sami cikakken ilimi mai inganci.
Okorocha ya ce: “Yanzu ina da yara sama da 25,000, kashi 75 daga cikinsu marayu ne kuma kusan kashi 15 daga cikinsu suna da mahaifi ne ko mahaifiya, kashi biyar sune wadanda ke rayuwa a talauci, duk da cewa iyayensu na raye.
“A wannan ranar zagayowar ranar haihuwata, na gayyaci yara daga sassa daban -daban na kasar, da kuma fadin Afirka.
Ya bayyana cewa da yawa daga cikin wadanda suka ci gajiyar gidauniyarsa sun kammala karatu suna aiki a fannoni daban -daban.
Ya bukaci ‘yan Najeriya da’ yan Afirka da su mara masa baya wajen fitar da karin yara daga kan titi tare da ba su ilimin da zai bunkasa nahiyar da inganta zaman lafiya.
Okorocha ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su ba gwamnati goyon bayan da ya dace wajen magance matsalar rashin tsaro, fashi da makami da sauran kalubalen da kasar ke fuskanta.
A cewar Okorocha “Wannan shine lokacin da ake matukar bukatar kafafen watsa labarai don tsaro da ci gaban kasar.
“Babu shakka al’ummarmu na cikin mawuyacin hali kuma akwai rashin tsaro da sauran kalubale. Wannan shine lokacin da za mu fi buƙatar ku, ”in ji shi.
Ya ce za a iya inganta Najeriya, idan kowa ya taka rawar da ta dace.
Wasu daga cikin yaran da gidauniyar sa ta yi wa rajista a makarantu daban -daban da suka zo yi masa murnar zagayowar ranar haihuwarsa sun fito ne daga Kenya, Congo, Kamaru, Mozambique, Gambia da Najeriya.
Wasu kuma sun fito ne daga Habasha, Laberiya, Burundi, Malawi, Sudan ta Kudu, Saliyo, Guinea Bissau, Nijar, Lesotho da Tanzania.
Wasu daga cikin ɗaliban, waɗanda suka zanta da NAN, sun gode wa Okorocha da ya ba su rayuwa da cikar buri ta hanyar ingantaccen ilimi.
Daya daga cikin daliban kwalejin Rochas Foundation College of Africa (ROFOCA), Miss Muna Begashaw daga Habasha, ta ce Okorocha ya ba ta kwarin giwa da wasu takwarorinta.
Ta bukaci wasu ‘yan Najeriya da sauran’ yan Afirka da su yi koyi da Okorocha ta hanyar taimakawa marasa galihu.
“Muna da miliyoyin marasa galihu a Afirka kuma mutum ɗaya ba zai iya kula da su duka ba. Muna buƙatar ƙarin mutane da za su yi koyi da shi, ”in ji Begashaw.
Wani dan Najeriya, Malam Sanusi Muhammed daga jihar Sakkwato kuma dalibi na aji biyu a babbar sakandare a ROFOCA Abuja, ya ce yayi matukar sa’ar kasancewa daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar Gidauniyar Rochas.
Muhammed ya ce gidauniyar ba wai ta ba su mafaka da abinci kawai ba, har da ingantaccen ilimi da tarbiyya don fuskantar kalubale a rayuwarsu. (NAN)