Jami’ar Bayero Kano ta nada wacce ta kafa cibiyar ci gaban manoman mata, Dakta Salamatu Garba, a matsayin shugabar kwamitin ba da shawara na bangaren masana’antu da sassa na cibiyar Noma ta yankunan Tsandauri ta jami’ar.
Nadin, wanda mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Haruna Musa ya amince da shi, na tsawon shekaru uku ne, domin jagorantar sabon kwamitin da aka sake tsarawa na cibiyar noma ta yankunan busassu.
A cikin wasikar da magatakardan jami’ar Haruna Aliyu ya sanya wa hannu, jami’ar Bayero Kano ta bayyana cewa nadin Dakta Salamatu Garba ya samo asali ne daga kwarewarta mai zurfi a fannin Noma da ci gaban al’umma, musamman wajen bunkasa Noma a yankunan busassu da tallafa wa kananan manoma.
Kwamitin ba da shawarar zai rika jagorantar cibiyar wajen daidaita shirye-shiryen horaswa, bincike da ci gaba da bukatun bangaren noma da masana’antu, tare da mayar da hankali kan kalubalen ci gaba da ke addabar yankunan busassu a Nijeriya.
Daga cikin ayyukan kwamitin akwai taimakawa cibiyar wajen ganowa da jawo kudaden tallafin bincike daga cikin Afirka da wajenta, karfafa hadin gwiwa da manyan masu ruwa da tsaki a bangaren noma na yankunan Tsandauri, da kuma tallafa wa shirye-shiryen da ke kara tasiri da amfanin ayyukan cibiyar.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa kwamitin ya kunshi manyan mutane daga bangarorin gwamnati da masu zaman kansu, ciki har da Magajin Garin Kano kuma daraktan gudanarwa na kamfanin Esoterra Investment Limited Alhaji Nasiru Wada, daraktan gudanarwa na kamfanin Dala Foods Nigeria Limited Alhaji Ali Safiyanu Madugu, wakilin kasa na cibiyar bunkasa takin zamani ta kasa da kasa Dakta Mohammed Salasi Idris, da daraktan gudanarwa na kamfanin Chimande Nigeria Limited Alhaji Yusuf Ado Kibiya.
Sauran mambobin sun hada da Dokta Donald Madukwe na kamfanin OCP, Abubakar Garba Ibrahim na kamfanin SILVEA International Limited, da Farfesa Jibrin M. Jibrin wanda tsohon daraktan cibiyar Noma ta yankunan Tsandauri, inda daraktan cibiyar zai kasance mamba kuma sakatare, yayin da mataimakan daraktoci masu kula da horaswa, bincike da yada labarai za su kasance mataimakan sakatarori.
Jami’ar ta bayyana yakinin cewa sabon kwamitin zai karfafa gudunmawar cibiyar wajen ci gaban noma mai dorewa a yankunan busassu.













































