Buhari ya tsawaita zamansa a Landan domin duba lafiyar haƙorinsa

346067515 974061587058890 5092858154002785879 n
346067515 974061587058890 5092858154002785879 n

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsawaita zamansa a Landan da mako guda domin duba lafiyar haƙoransa, kamar yadda mai magana da yawunsa Femi Adesina ya bayyana.

Shugaban na Najeriya dai ya je Landan ne domin halartar bikin naɗin sarkin Ingila, charles lll.

Tun da farko an tsara cewa shugaba Buhari zai koma Najeriya a cikin wannan mako, to sai dai yanzu zai ƙara mako guda domin ganawa da likitan haƙoransa, wanda tuni ya fara duba shi.

”Likitan nasa ya buƙaci ya ƙara ganinsa nan da kwana biyar domin ci gaba da lura da yanayin haƙoran nasa”, kamar yadda Femi Adesina ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar.

Tun bayan da ya ɗare kujerar shugabancin Najeriya, shugaba Buhari na yawan zuwa Birtaniya kan dalilai na rashin lafiyar da ba a bayyanawa.

A ranar 29 ga watan Mayu ne zai miƙa mulki ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu, bayan kammala wa’adi biyu na mulkinsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here