Boko Haram sun kashe mazauna wani ƙauyen Borno su 15

b2fd3e01 1bef 4c90 aed3 28182bf931c8
b2fd3e01 1bef 4c90 aed3 28182bf931c8

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe aƙalla mutane 15 a hare-haren haɗin gwiwa da suka kai wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Jere ta jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kai farmaki ne ƙauyen Kofa cikin tsakar dare inda suka fara harbe-harbe, wanda ya dauki kimanin sa’a guda.

An samu labarin cewa sun kuma kai hari a Molai Kura da Molai Gana, inda suka yi wa wasu mutane yankan rago.

An ba da rahoton cewa mazauna yankin da dama sun tsere daga gidajensu don samun mafaka a cikin daji.

Wani jigo a ƙungiyar ’yan sintiri, Bukar Ali Musty, ya ce manoma na aikin gonakinsu a ƙaramar hukumar Jere cikin jihar Borno ne, a lokacin da “‘yan ta’addan suka kai musu hari” tare da sare musu kai.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here