Binciken albashin ƙananan hukumomi ya bankado badakalar Naira miliyan 28 a Kano

Abba Kabir Yusuf Kano Kano 715x430

Gwamnatin jihar Kano ta bankado wata badaƙala a cikin albashin watan Maris na 2025, wanda ya kai ga kwato sama da Naira miliyan 28 daga asusun kananan hukumomi.

SolaBase ta ruwaito cewa an bayyana hakan ne a wata sanarwa da Musa Tanko Muhammad, sakataren yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar, ya fitar ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, gano hakan na daga cikin kokarin da jihar ke yi a karkashin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na sake fasalin tsarin albashi a cikin ma’aikatan gwamnati.

Karin karatu: Ranar yaƙi da zazzabin cizon sauro ta duniya: Kano ta sake jaddada aniyarta na kawar da cutar zazzabin cizon sauro

A cewar sanarwar, a kwanan baya ne aka kafa kwamitin Biyan Kudaden da zai kula da sauye-sauye, kuma a shirye-shiryen gudanar da cikakken aikin sa, ya umurci dukkan ma’aikatu da hukumomi da ƙananan hukumomi da su sake duba takardun biyan albashin da aka buga a watan Maris na 2025.

A kokarin tabbatar da aikin ya bankado wata matsala da ta kunno kai a tsarin biyan albashi na ƙananan hukumomi, inda har yanzu mutane 247 da suka yi ritaya ko kuma suka mutu ke karbar albashi, wanda adadin kuɗin da ake cirewa na karya ya kai Naira 27,824,395.40 a watan Maris ɗin 2025 kaɗai.

Tuni dai gwamnati ta kwato kudaden tare da mayar da su asusun kananan hukumomin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Sanarwar ta jaddada kudirin gwamnatin na tabbatar da gaskiya da rikon amana da kuma kula da dukiyar al’umma, inda ta sha alwashin cewa duk wadanda ke da hannu a zamba zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here