Bauchi: Jami’an NSCDC sun cafke babbar mota ɗauke da ƙarafan titin jirgin ƙasa

Stolen Railway Slippers Concealed In Loads Of Sawdust 750x430

Tawagar jami’an hukumar tsaro ta Civil Defence wadanda ke lura da fannin hakar ma’adanai sun kama wata babbar motar dakon kaya dauke da manyan karafan titin jirgin kasa a yankin karamar hukumar Missu ta jihar Bauchi.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama’a na hukumar sifurin jiragen kasa NRC, Yakub Mahmood ya fitar.

Manajan Daraktan hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa Dakta Kayode Opeifa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a jiya Talata, inda ya ce, an cafke motar ne a ranar 20 ga watan nan da muke ciki na Yuni.

Haka kuma ya kara da cewa, an boye karafan ne a karkashin buhunan ciyayi, lamarin da ya janyo zargin boye wa da gangan da kuma lalata dukiyar gwamnati .

Ta cikin sanarwar, Opeifa ya tabbatar da cewa an kama mutane uku da ake zargi, kuma motar da kayayyakin suna hannun hukumar tsaron ta Civil Defence domin ci gaba da bincike.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here