Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta umarci tsohon shugaban kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC), Mele Kyari, da ya riƙa halartar hedkwatar hukumar da ke Abuja kullum, yayin da ake shirin gurfanar da shi da wasu a gaban kotu nan ba da jimawa ba.
Rahotanni sun ce, binciken hukumar ya shafi sama da Dala biliyan 2.5 da aka kashe a gyaran matatun mai huɗu na ƙasar.
Hakan ya sa EFCC ke buƙatar Kyari ya bayyana kullum domin amsa tambayoyi da fayyace takardu da kuma bayanan kwangiloli.
Majiyoyi sun ce wasu tsoffin shugabannin matatun mai da ma’aikatan NNPC da kwangiloli da dama sun riga sun bayyana a gaban masu bincike, inda tambayar Kyari ita ce mataki na ƙarshe don kammala binciken.
Labari mai alaƙa: Yanzu-yanzu: Mele Kyari ya bayyana a Hedikwatar EFCC
Daga cikin kuɗaɗen da ake bincike shi akwai Dala biliyan $1.55 da aka ware wa matatar mai ta Port Harcourt sai Dala miliyan 740.6 ga matatar Kaduna, da kuma dala miliyan 656.9 ga matatar Warri.
Duk da haka, majiyoyin sun ce Kyari ya ce ba shi da abin ɓoyewa.
Tun daga 2010 an kashe fiye da Dala biliyan 18 kan gyaran matatun mai, amma har yanzu suna cikin matsala.
Duk da kwangiloli da dama da aka bayar, ciki har da na Daewoo Engineering and Construction Limited da Saipem Contracting Nigeria Limited, matatun ba su fara aiki yadda ya kamata ba.
Ana sa ran Kyari da wasu tsoffin manyan jami’an NNPC za su fuskanci shari’a bisa hujjojin da aka tattara, kuma a kotu za a tabbatar da gaskiya ko akasin haka.












































