Badaƙalar Albashi: Gwamnatin Katsina ta kori ma’aikata 3,488

Gov Radda (1)

Gwamnatin jihar Katsina ta kori ma’aikata 3,488 daga kananan hukumomi 34 da kuma hukumomin ilimi na kananan hukumomi, bayan tantancewar na’ura wadda ta bankado manyan matsaloli na badakalar albashi.

Gwamna Dikko Radda ya karɓi rahoton kwamitin a ranar Laraba, inda aka bayyana cewa daga cikin ma’aikata 50,172 da aka tantance, an tabbatar da sahihancin 46,380, yayin da sauran aka gano da takardun bogi, ma’aikatan bogi, rashin zuwa aiki ko kuma sam babu su amma suna karbar albashi.

Rahoton, wanda aka gabatar a zaman majalisar zartarwa ta jiha, ya nuna cewa aikin ya samar da kundin bayanai na zamani na farko a tarihin jihar kan ma’aikatan kananan hukumomi da ma’aikatan ilimi na kananan hukumomi, tare da hasashen adana kuɗin albashi har Naira miliyan 453.3 a duk wata idan an aiwatar da shawarwarin.

Kwamitin ya gano takardun haihuwa na bogi, ɗaukar ma’aikata ƙasa da shekaru, karin girma ba bisa ƙa’ida ba, da kuma ma’aikatan da ke ba da mukamansu ga wasu.

Karin labari: Shekarun haihuwa na bogi: Rundunar ‘yan sanda za ta gurfanar da tsohon mataimakin sufeto janar da kwamishinoni biyu masu ritaya

Haka kuma an kwato Naira miliyan 4.6 daga jami’an da ke karɓar albashi sau biyu ko suna karɓar kuɗi duk da suna hutun aiki.

Shugaban kwamitin, Abdullahi A. Gagare, ya bayyana cewa an kama sakataren ilimi na hukumar ilimin kananan hukumomi LEA ta Zango da hannu wajen saka ma’aikata 24 na bogi, abin da ya kira.

Gwamna Radda ya ce ya san wannan aiki na iya cutar da siyasarsa, amma ya yi hakan ne domin gyaran tsarin jihar.

Ya kuma bayyana cewa yanzu haka kananan hukumomi sun tara kusan rabin biliyan, wanda zai iya kaiwa Naira biliyan 5.7 idan aka aiwatar da shawarwarin.

Radda ya kara da cewa, duk da samun kuɗaɗen shiga masu yawa, wasu kananan hukumomi kamar Kafur, Malumfashi da Daura na fama da nauyin albashi saboda cunkoson ma’aikatan da ba na gaskiya ba.

Ya ce rage wannan nauyi zai buɗe damammaki domin ci gaban ƙauyuka, yana mai jaddada cewa “na yi haka ne domin kuɗi su shiga aikin al’umma gaba ɗaya, ba hannun ‘yan tsiraru ba.”

Kwamitin mutum 10 da ya gudanar da aikin ya ƙunshi tsoffin manyan sakatarori hudu, daraktoci shida, tare da ƙarin mambobi 16 da jami’an tsaro a matsayin masu tallafi.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here