“Babu wanda zai rasa aikinsa lokacin haɗe hukumomin gwamnati” – Mohammed Idris

Mohammed Idris, minista, yada labarai, rasa, aiki, hukumomin, gwamnati
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na Najeriya, Mohammed Idris, ya ce babu ma'aikacin da zai rasa aikinsa wajen aiwatar da rahoton Oronsaye, wanda...

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na Najeriya, Mohammed Idris, ya ce babu ma’aikacin da zai rasa aikinsa wajen aiwatar da rahoton Oronsaye, wanda ke neman a haɗe ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya.

Idris ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Laraba a taron manema labarai karo na hudu na ministoci.

“Abin nufi shi ne gwamnati na son rage tsadar kayayyaki da kuma inganta yadda ake gudanar da ayyuka. Ba wai yana nufin gwamnati na shirin korar ma’aikata ko jefa mutane cikin kasuwar kwadago ba,” inji shi.

Karin labari: ‘Ƴan sanda sun kama mahaifin da ya harbe ɗansa kan abinci a Abiya

Ministan ya ce aiki da rahoton wata alama ce karara ta jajircewar shugaba Tinubu na yin taka-tsantsan a kasafin kudi da gudanar da mulki ta hanyar yin nazari mai zurfi a kan kwamitocin gwamnati da hukumomi da ma’aikatun gwamnati.

Ya ce amincewa da yin aiki da rahoton na Orosanye, wanda ya biyo bayan nazari mai zurfi, shi ne tabbatar da cewa ba’a yi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyuka masu muhimmanci, sannan kuma a magance bukatun ‘yan kasa yadda ya kamata tare da sanya bukatun al’umma a gaba.

Karin labari: Benin za ta aika da jami’an tsaro sama da 1,000 zuwa Haiti

“Ta hanyar aiwatar da rahoton Oronsaye, shugaba Tinubu yana da niyyar cimma babban tanadin farashi ta hanyar kawar da kwafin ayyuka da daidaita tsarin gudanarwa, da inganta rabon albarkatu.”

Wannan tsari na sa ido zai ba wa gwamnati damar gudanar da aiki yadda ya kamata tare da kiyaye inganci da isar da ayyuka ga al’ummar Najeriya,” inji shi.

Ministan wanda ya ce ‘yan Najeriya sun fara ganin alfanun sauye-sauyen da shugaban ƙasa ke jagoranta a sassa daban-daban, ya jaddada cewa rahoton da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar na nuni da cewa Najeriya ta samu ƙaruwar kuɗin da ake samu a cikin ƙasa da kashi 3.46 cikin 100.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here