Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce babu laifi a yi tsarin jam’iyya daya a Najeriya.
Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Juma’a bayan ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar dattawa uku daga jihar Kebbi domin ganawa da shugaba Bola Tinubu.
Sanatoci uku – Adamu Aliero, Yahaya Abdullahi da Garba Maidoki – a karkashin jam’iyyar PDP, sun bayyana aniyarsu ta komawa APC.
Da yake mayar da martani kan ko guguwar sauya shekar ‘yan siyasan adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki ba za ta jefa Najeriya cikin jam’iyya daya ba, Ganduje ya ba da misali da kasar Sin a matsayin ƙasa mai jam’iyya daya.
Labari mai alaƙa: Sanatoci daga jihar Kebbi sun koma APC bayan sun gana da shugaba Tinubu
“Mun zo nan ne domin shugaban kasa ya albarkaci wannan kudiri, kuma shugaban ya albarkaci wannan kudiri. A ranar Talata, ina rokon ku da ku je ku ga abin da zai faru a zauren majalisa,” inji shi.
“Kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka fi karfi a duniya, kuma tsarin jam’iyya daya ne, ba wai muna cewa muna aiki ne don tsarin jam’iyya daya ba, amma idan wannan shi ne burin ‘yan Najeriya, ba za mu iya yin jayayya da hakan ba.”