IGP ya gayyaci mai magana da yawun gwamnan Kano bisa ƙorafin Ganduje

IGP Kayode Egbetokun PMF 750x430 (1)

Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun, ya umarci rundunar bincike ta kwamitin kula da ayyukan ‘yan sanda da ta kai mai magana da yawun gwamnan kano Sunusi Bature Dawakin-Tofa zuwa shelkwatar hukumar ta kasa domin amsa tuhumar batanci da ake masa kan kitsa dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje daga jam’iyyar.

A shekarar 2024, kwamitin zartarwa na jam’iyyar APC a mazabar Ganduje ya dakatar da Ganduje daga jam’iyyar, bisa zargin cin amanar jam’iyyar da kuma rashin biyan kudin mambobin su.

Ana dai zargin Sunusi Bature Dawakin Tofa da jagorantar dakatar da Ganduje, kasancewarsu ‘yan karamar hukuma daya.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 23 ga watan Mayun bana mai dauke da lamba: CR/3000/IGP-SEC/MU/ADM/14/ABJ/VOL 118/57 wadda aka aike wa sakataren gwamnatin jihar Kano, Kayode Egbetokun ya bukaci Sunusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana a gaban SP Mojirode Obisiji a ranar Alhamis 29 ga watan mayun da ya gabata.

Bayan haka, haka ne wata babbar kotu ta bayar da umarnin hana sufeto Janar na ‘yan sanda da hukumar DSS da sauran jami’an tsaro kama Sunusi Bature Dawakin-Tofa.

Hukuncin wucin gadin, wanda aka bayar a ranar 12 ga Disamba, 2024, ya kare Sunusi Bature Dawakin-Tofa daga tsangwama, tsarewa da kuma tsoratarwa daga jami’ai ko kuma babban Sufeton har ma da jami’an DSS da sauran hukumomin tsaro.

An kuma ba da umarnin ga Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda AIG na shiyya ta daya da kwamishinan ‘yan sandan Kano da SP Mojirade Obisiji da DCP Akin Fakorede da jami’an tsaron farin kaya da sauran jami’an tsaron Najeriya da dai sauransu.

A cewar kara mai lamba K/M2500/2024, umarnin kotun ya haramta duk wani mataki da zai iya cin karo da muhimman hakkokin Dawakin-Tofa na ‘yanci da mutunci da kuma walwalarsa.

Rikici tsakanin NNPP da APC a Kano kafin 2027 ya ta’allaka ne kan siyasar cikin gida a mahaifar Ganduje wanda ya kuduri aniyar sanya dansa “Abba Ganduje” da kuma rikicin masarautar Kano tsakanin sarakunan Kano na 14 da 15, inda Abdullahi Ganduje da Sanusi Bature suka shiga tsakani, kowa na kokarin yin nasara a kan abokin karawarsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here