Babban Malamin Addini mai bada Fatawa a ƙasar Saudiyya, Abdulaziz al-Sheikh, ya rasu yana da shekaru 82

Saudi Grand Mufti Sheikh Abdulaziz Al Sheikh e1758623758551

Babban malamin addinin Musulunci kuma mai bada Fatawa na ƙasar Saudiyya, wanda shi ne Grand Mufti, Sheikh Abdulaziz al-Sheikh, ya rasu yana da shekaru 82 a duniya.

Fadar Sarki ta ƙasar Saudiyya ce ta sanar da rasuwarsa a ranar Talata, abin da ya nuna ƙarshen wani zamani a shugabancin addini na ƙasar.

Tun daga shekarar 1999 yake rike da wannan mukami mai girma a masarautar.

A sanarwar, Fadar Sarki ta bayyana cewa: “Masarautar da ma duniya ta Musulmi sun yi babban rashi na ƙwararren malami, wanda ya bayar da gudummawa ta musamman wajen cigaban ilimi, Musulunci da Musulmai.” Jana’izarsa za a gudanar da ita a babban birnin Riyadh da sauran masallatai a fadin kasar nan gaba a yau.

Grand Mufti a kasashen Musulmi shi ne ke fassara dokokin shari’a tare da bayar da fatawa, wato hukunci na addini.

Sheikh Abdulaziz al-Sheikh ya yi tasiri sosai a wannan fanni, musamman a lokacin da Saudiyya ke bin tafarkin tsattsauran akidar Wahhabi kafin fara sassauta wasu dokoki.

Tun lokacin da Yariman Gadi Mohammed bin Salman ya fara jawo kasar zuwa ga manufar “Musulunci na matsakaici”, an ragu da tasirin malamai masu tsattsauran ra’ayi.

Sai dai Sheikh al-Sheikh ya kasance mai ra’ayi mai tsauri a fannoni da dama.

A 2011 ya yi adawa da daukar mata aiki a shaguna, yana kiran hakan da “laifi da rashin mutunci.”

Amma daga baya ya yabawa Sarki Abdullah lokacin da ya bai wa mata damar tsayawa takarar kujerar kananan hukumomi da shiga majalisar dokoki.

Rasuwar Sheikh Abdulaziz al-Sheikh ta bar gibi a shugabancin addinin Saudiyya, inda al’umma a ciki da wajen masarautar ke tunawa da irin tasirin da ya yi a rayuwarsu da addini.

dpa/ NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here