Gwamnan babban bankin Najeriya na CBN, Yemi Cardoso ya sanar da ƙarin kuɗin ruwa zuwa kashi 22.75 cikin ɗari daga kashi 18. 75 cikin ɗari a bara.
Cardorso ya bayyana hakan ne bayan kammala taron manufofin kuɗaɗe na ƙasar na farko tun bayan zamansa shugaban CBN, da aka yi a Abuja a ranar Talata.
Karin labari: Fada da ’Yar Sanda ya kai wata matashiya gidan Yari
Mista Cardoso ya ce an dauki wannan matakin ne da manufar dakile hauhawar farashi da kasar ke fama da shi.