Ba zan taɓa barin siyasa ba, haɗin kai na gaskiya na jam’iyya ne, ba na ƙashin kai ba – Shekarau

WhatsApp Image 2025 11 05 at 16.55.01 750x430

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa zai ci gaba da kasancewa cikin harkokin siyasa har karshen rayuwarsa, yana mai jaddada muhimmancin samar da haɗin kai na jam’iyyu bisa manufa kafin babban zaɓen 2027.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Shekarau ya bayyana hakan ne a wani taron hira da ’yan jarida da ya gudanar a Kano a ranar Laraba, a cikin bukukuwan cikar shekarunsa 70 da haihuwa.

Ya ce irin hadin kan da zai iya kalubalantar jam’iyya mai mulki a 2027 dole ne ya kasance na jam’iyyu da aƙida, ba na son rai ko mutum ɗaya ba.

Ya kuma tunatar da yadda jam’iyyun ANPP, ACN, CPC da wani bangare na APGA suka hade suka kafa jam’iyyar APC a shekarar 2013 a matsayin misali na hadin kai na gaskiya.

Shekarau ya kara da cewa idan mutane suka bar jam’iyyunsu don su hade da wasu ba tare da tsarin jam’iyyun su ba, hakan ba zai taba zama hadin kai na siyasa na hakika ba.

Tsohon ministan ilimi kuma sanata, wanda yanzu jagora ne a jam’iyyar PDP, ya bukaci jam’iyyun adawa su hade su kafa jam’iyya mai ƙarfi guda idan suna son ƙwace mulki a 2027.

Ya ce duk da matsalolin da PDP ke fuskanta, ita ce kadai jam’iyyar da ta tsira tun daga 1998, yana kuma kira ga jam’iyyun ADC, Labour da SDP da su hada kai da PDP domin ceto kasar daga matsalolin tattalin arziki da tsaro.

Shekarau ya bayyana cewa ba zai taba yin ritaya daga siyasa ba domin siyasa hidima ce ga al’umma, don haka zai ci gaba da bayar da gudunmawa matukar yana da rai.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu da ta kara kaimi wajen magance matsalolin tsaro da tabbatar da wadataccen abinci, yana mai cewa samun abinci mai sauƙi shi ne ginshikin zaman lafiya da ci gaban jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here