“Ba za mu biya ƴan bindiga ko sisin kwabo ba” – Tinubu

Tinubu, Shugaban, Najeriya, sojoji, kudancin, hukunta, alkawari
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi alƙawarin hukunta mutanen da ke da hannu a kisan sojoji 14 ranar 14 ga watan Maris a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umarci jami’an tsaro da kada su biya kuɗin fansar sakin kusan ɗalibai 300 da malaminsu da aka yi garkuwa da su makon da ya gabata daga wata makaranta da ke Kaduna a yankin arewa maso yammacin ƙasar.

Tinubu ya kuma umarci hukumomin tsaro da su tabbatar an kuɓutar da dukkan mutanen da aka sace ba tare da biyan ƴan bindigar kuɗin fansa ba, kamar yadda ministan yaɗa labarai, Muhammed Idris ya shaidawa ƴan jarida a ranar Laraba.

Karin labari: Najeriya ta samu dala biliyan 1.3

Ministan ya ce shugaba Tinubu ya faɗa wa sojojin da ke laluben inda ɗaliban suke su tabbatar ba’a biya ko sisin kwabo ba.

Tun farko, ƴan’uwan ɗaliban da ke tsaren sun ce ƴan bindiga sun buƙaci a biya su kuɗi mai yawa domin su saki yaran da suka sace daga makarantarsu a ƙauyen Kuriga.

Cikin makon da ya gabata, an sace mutane da dama ciki har da fiye da mutum 60 daga wani ƙauye a dai jihar ta Kaduna.

Karin labari: Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu ya bude iyakoki

Cikin shekara uku da ta gabata, ɗaruruwan ɗalibai aka sace, wasu a cikinsu an sake su bayan tattaunawa da hukumomi duk da cewa jami’ai sun musanta biyan kuɗin fansa.

Wata doka da aka amince da ita a shekarar 2022 ta hana biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa.

Ƙaruwar sace-sacen mutane na zama ƙalubale ga gwamnatin Tinubu da ta yi alƙawarin magance matsalar tsaro.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here