Hukumar ‘yan sandan farin kaya a Najeriya ta DSS ta tabbatar da gayyatar tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari zuwa ofishinta.
Sai dai hukumar ba ta faɗi dalilin da ya sa ta gayyace shi ba, tana mai musanta “jita-jitar” da ake yaɗawa cewa an tsare shi ne saboda ya ƙi amsa wayar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
A ranar Asabar ne wasu rahotanni da aka wallafa a shafukan intanet suka ce DSS ta kama tsohon gwamnan ne saboda ya ƙi sauraron shugaban ƙasar game da zaɓen shugaban Majalisar Dattawa da aka yi a watan da ya gabata.
DSS ta bayyana labarin a matsayin “na ƙarya” kuma “abin dariya”.
“Abu ne maras amfani ko kuma na dariya….Wannan shi ake kira shashanci a rahoto. Yari ya san dalilin da ya sa aka gayyace shi,” a cewar sanarwar da DSS ta wallafa a shafinta na Twitter.













































