Ba mu da niyyar ƙara farashin fetur zuwa N700 a Najeriya – IPMAN

IPMAN
IPMAN

Ƙungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu a Najeriya da kuma masu dakon man sun musanta yunƙurin ƙara farashin man zuwa N700 kan lita ɗaya.

Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN) ta masu kasuwancin mai da kuma Distributors and Transporters of Petroleum Products (ADITOP) sun musanta shirin ne cikin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Asabar.

Suka ce farashin mai a yanzu yana tafiya ne kan farashin kasuwa, kuma an yi hasashen ƙara kuɗin man ne saboda darajar naira da ke sama tana ƙasa a kasuwar canji.

A cewar rahoton NAN, wasu ‘yan kasuwa sun yi hasashen tashin farashin man ne zuwa naira 700 kan kowace lita, saɓanin yanzu da yake 540, da zarar ‘yan kasuwa masu zaman kansu sun fara shiga da man cikin ƙasar a watan Yuli.

Sun yi hasashen ne bisa farashin da kasuwa ta yi wa naira a yanzu da kuma kuɗin sauke man a Najeriya.

Darajar naira ta ragu a ranar Juma’a zuwa N769.25 kan dala ɗaya a buɗaɗɗiyar kasuwar canji, bayan Shugaba Bola Tinubu ya janye tsarin ƙayyade farashin naira da Babban Bankin Najeriya ke yi a baya.

Hakan na nufin darajar nairar ta ragu da kashi 0.82 cikin 100 idan aka kwatanta da N763 da aka canzar da ita kafin fara bikin Babbar Sallah a ranar Laraba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here