Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mayar da martani kan faduwar da ya yi lokacin bikin ranar dimokuraɗiyya ta 12 ga watan Yunin 2024.
Bidiyon faduwar shugaban ya yaɗu a shafukan sada zumunta wanda ya nuna Tinubu a lokacin da yake yunkurin shiga motar faretin a dandalin Eagle Square da ke Abuja inda ya rasa wani mataki wajen hawar motar ya faɗi.
Tinubu mai shekaru 72, ya ce dimokraɗiyya ta cancanci faduwa.
Karin labari: Yan sanda sun kama wani mutum da sassan jikin dan Adam
Da yake magana game da abin da ya faru a ranar Laraba, shugaban ya yi dariya da cewa “na rusuna ne don girmama dimokuraɗiyya a salon Yarbawa.”
Shugaba Tinubu ya kuma yi amfani da taron liyafar cin abincin na bikin dimokuraɗiyya wajen kira ga hadin kan Nijeriya, ba tare da la’akari da kabila ko addini ko siyasa ba.
Ya kuma jaddada cewa hadin kan Najeriya ba abu ne da za a iya yin cinikinsa ba.
Bayan afkuwar lamarin, an samu martani da dama daga ‘yan Najeriya daban-daban ciki har da ‘yan adawa.