Atiku ya musanta cewa ya bai wa jami’in sojan ruwa mota ƙirar SUV saboda rikicinsa da Wike

Atiku Abubakar 750x430
Atiku Abubakar, Nigeria's main opposition presidential candidate, gestures during a Bloomberg Television interview in Lagos, Nigeria, on Wednesday, Jan. 16, 2018. Abubakar said he'll sell the state oil company, which he called a "mafia organization," and attract private investors to drive growth and create jobs if he wins office next month. Photographer: George Osodi/Bloomberg via Getty Images

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da ke cewa ya ba Laftanar Ahmed Yerima, jami’in sojan ruwa da ya samu saɓani da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, sabuwar mota kirar Toyota SUV.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ta shafin X a ranar Alhamis, ya bayyana cewa labarin da ake yadawa a kafafen sada zumunta ƙarya ne gaba ɗaya, kuma ba shi da wata hujja ko tushe.

Sanarwar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da labarin da aka ƙirƙira, tana mai jaddada cewa Atiku bai ba Yerima, ko wani mutum dabam, wata mota ba.

Wannan zargin ya samo asali ne daga wani labarin da ya yadu a Facebook a ranar Laraba, inda aka ce Atiku ya ba jami’in sojan ruwa kyauta saboda saɓaninsa da Wike kan wani filin gwamnati da ake taƙaddama a Abuja.

Rahotanni sun ce, rikicin ya faru ne a ranar Talata lokacin da Wike ya fuskanci wani jami’in soja mai suna Laftanar Yerima yayin duba wani fili da ake gardama a unguwar Gaduwa a babban birnin tarayya.

Bidiyon lamarin da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna musayar yawu mai zafi tsakanin ministan da jami’in, wanda ya dage cewa yana kare mallakar rundunar sojan ruwa.

Wannan lamari ya jawo martani daga jama’a da dama, ciki har da tsohon babban hafsan sojojin ƙasa, Janar Tukur Buratai mai ritaya, da wasu ’yan siyasa, waɗanda suka nemi a nuna ladabi da mutunta hukumomi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here