Ƙungiyar malamai ta jami’o’i ta Kano ta bayyana matsanancin damuwa kan jinkirin gwamnatin Tarayya wajen sake tattaunawa kan yarjejeniyar inganta tsarin jami’o’in gwamnati a ƙasar nan.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ƙungiyar ta fitar da wannan gargadi a taron manema labarai da aka gudanar a ofishinta da ke jami’ar Bayero Kano.
Ƙungiyar ta ƙunshi jami’o’i da dama ciki har da jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, jami’ar Bayero Kano, jami’ar jihar Kaduna, jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, jami’ar tarayya ta Dutse, jami’ar Northwest da ke Kano da jami’ar Sule Lamido da ke Kafin Hausa.
Shugaban kungiyar, Abdulkadir Muhammad, ya bayyana cewa bayan taron kwamitin zartarwa na ƙasa da aka gudanar a ranar takwas da tara ga watan Nuwamba a jami’ar jihar Taraba, mambobin sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ke ƙara nuna sakaci wajen cika alƙawurran da ta riga ta ɗauka.
Ƙungiyar ta ce ta taɓa shiga yajin aikin gargadi na makonni biyu a watan Oktoba domin ba gwamnati dama ta shiga tattaunawa mai inganci, amma abin da ya biyo baya ya nuna cewa babu wani ci gaba da ya kamata a dogara da shi.
Ta ƙara da cewa duk da ƙaramin yunƙurin gwamnati na biyan wasu bashin ƙarin girma da biyan wasu takardu saboda hauhawar farashi, matsaloli na manyan al’amura irin su jin daɗin malamai, ingancin aiki da dakile ficewar ƙwararru daga ƙasar nan ba su samu kulawa ba, lamarin da ka iya jawo sake rufe jami’o’i idan wa’adin wata guda da suka bayar ya ƙare ba tare da an magance su ba.













































