ASUP ta bawa gwamnatin tarayya wa’adin kwana 15 don warware buƙatun ta
Kungiyar Malaman Makarantun Kimiyya da Fasaha (ASUP) ta bayar da wa’adin kwanaki 15 ga Gwamnatin Tarayya domin ta magance bukatun ta daban-daban.
Shugaban kungiyar ASUP na kasa Mista Shammah Kpanja ne ya fitar da wa’adin lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa (NEC) a Abuja.
Kpanja ya ce matakin da kungiyar ta dauka ya zama wajibi domin har yanzu gwamnatin tarayya ba ta aiwatar da wasu muradan dasuka shafi fannin bukatun su ba.
“Kungiyarmu ta bayar da wa’adin kwanaki 15 kamar yadda doka ta tanada daga ranar 7 ga Oktoba ga masu mallakar manyan makarantun gwamnati don magance wadannan abubuwan.
“A karshen wa’adin, hukumar za ta sake zama domin daukar mataki na gaba da kuma tsara yadda za a magance matsalolin da aka lissafa.
Ya ce bukatun sun hada da sake duba tare da mayar da duk wasu ayyukan da ba su dace da tanadin dokar Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da sauran kayan aikin gudanarwa na bangaren mulki.
Ya yi kira da a gaggauta fara aikin sake duba takardar da aka dakatar mai suna Schemes of service for Polytechnics 2023 kamar yadda aka amince a taron uku na Yuli 2024.