APC ta musanta yunƙurin dakatar da shirin tattara sakamakon zabe a zamanan ce

APC Convention
APC Convention

Kwamutin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ta musanta zargin cewa gwamnatin tarayya na matsin lamba ga hukumar zabe ta kasa kan ta dakatar da watsa sakamakon zabe ta hanyar zamani a shekarar 2023.

Daraktan yada labarai na musamman kan ayyuka da sabbin kafafen yada labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC Mista Femi Fani-Kayode ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja.

‘Yan adawar sun yi zargin cewa Gwamnatin Tarayya na matsin lamba ga hukumar zabe kan dakarar tsarin tantance masu kada kuri’a daga runbun adana sakamako gabanin zabe.

Sai dai Fani-Kayode ya ce duk wannan ba gaskiya ba ne.

“Su ne wadanda suka rasa gwamnoni biyar, kuma ba za su iya sa shugabannin jam’iyyar su, su zo taronsu a bikin rantsar da shugabannin su ba.

“Ba mu da wannan kalubale, muna aiki cikin natsuwa amma tabbas, a matsayinmu na bishiya guda ina matukar alfaharin da wannan,” in ji shi.

Fani-Kayode ya ce taron wanda har ila yau ya samu halartar daraktocin yada labarai na jam’iyyar guda hudu, ya fayyace duk wasu matakai da suka shafi fara yakin neman zaben shugaban kasa a 2023.

Mista Festus Keyamo, wanda shi ne mai magana da yawun jam’iyyar APC yayin da yake maida martani kan zargin, ya ce sam babu wani lokaci da jam’iyyar ko dai ta kwamitin gudanarwar ta na kasa dake matsin lamba ga INEC. .

Ya ce wadanda ke ganin sune zasu sha kaye a zaben 2023 ne ke yin irin wannan zargin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here