An shiga ruɗani bayan kisan limami a Zamfara

Abubakar, Mada, kisan, limami, jihar, zamfara
Al'ummar garin Mada da ke Gusau a jihar Zamfara sun shiga wani hali bayan sun wayi gari da labarin mutuwar limamin masallacin garin, Abubakar Hassan Mada...

Al’ummar garin Mada da ke Gusau a jihar Zamfara sun shiga wani hali bayan sun wayi gari da labarin mutuwar limamin masallacin garin, Abubakar Hassan Mada.

Wasu mazauna garin sun bayyana cewa an tsinci gawar limanin ne, bayan wasu da ake zargin wadansu sanye da kayan sabuwar rundunar tsaron jihar sun tafi da shi a ranar Talata.

Sai dai bayan wani lokaci an tsinci gawar malamin bayan an yi masa yankan rago.

Karin labari: Shugaban jam’iyyar APC Omotoso ya rasu

Ɗaya daga cikin mutanen garin na Mada ya shaida cewa “Jiya da yamma bayan sallar la’asar wasu sanye da kaya irin na asakarawa suka shigo, an ce mana daga yankin Tsafe su ke, sai suka haɗu da askarawa na nan Mada, suka nuna musu gidan liman Abubakar Hassan Mada,”

Ya ƙara da cewa “Bayan da suka fita da shi wajen gari sai suka tsaya suka yi masa yankan rago.”

Mutum na biyu wanda shi ma mazaunin garin na Mada ne ya ce, “sun zo sun tafi da shi har suna dariya suna raha, ba mu yi tunanin wani abu ne maras kyau zai faru da shi ba.”

Karin labari: Hukumar NSCDC ta kama wanda aka kora bisa zargin badakalar bisa

Sai dai a nasu ɓangaren, rundunar Askarawar Zamfara sun bayyana cewa suna bincike kan kisan malamin.

Kwamandan Askarawan Zamfara, Kanar Rabiu Ƴandoto mai murabus ya ce ya zuwa safiyar ranar Laraba hukumar ta fara bincike a kan lamarin.

A cewarsa “Mun sa a tattara dukkanin Askarawan yankin Mada domin yin bincike game da kisan limamin.”

Karin labari: Daurawa Ya Shiga Ofis Bayan Dawowarsa Hisbah

Sai dai ya bayyana cewa doka ba ta bai wa wani ba’askare damar ɗaukar doka a hannunsa ba, koda kuwa ya kama wanda ake zargi da laifi.

Mada na cikin yankunan jihar Zamfara da suke fama da mummunar matsalar ‘ƴan fashin daji masu kashewa tare da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here