An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a jihar Adamawa

Governor of Adamawa State Ahmadu Fintiri
Governor of Adamawa State Ahmadu Fintiri

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya ayyana dokar ta-ɓaci ta tsawon sa’a 24 a fadin jihar.

Cikin wani saƙon da gwamnan ya wallafa a shafinsa ta twitter, ya ce an sanya dokar ne sakamakon ƙaruwar hare-haren da ɓata-gari ke kai wa mutane da kasuwanni a faɗin jihar.

Rahotonni daga jihar sun ce wasu ɓata-gari ne suka riƙa far wa mutane da makamai a birnin Yola tare da sace musu dukiyoyi a shagunansu.

Gwamna Fintiri ya ce an hana zirga-zirga a jihar, sai iya mutanen da ke ayyuka na musamman, waɗanda ke ɗauke da katin shaidar aiki.

Gwamnan wanda ya yi kira ga al’ummar jihar da su yi biyayya ga dokar, ya ce tsaron lafiyar mutanen jihar shi ne babban abin da ya sanya a gaba.

Wani mazaunin Yola mai suna Aminu Yakubu ya shaida wa BBC cewa wasu matasa maza da mata ne suka fito a garin Jimeta, tare da aɓkawa rumbunan ajiye abinci, inda suka yi ta ɗiban kayan abinci daban-daban irin shinkafa da taliya da sauransu.

Ya ce jami’an tsaro sun yi amfani da karfi kan mutanen ne bayan da suka nuna turjiya.

Ya kuma ce jami’an tsaro sun kama mutane da dama kan lamarin, tare da tafiya da su domin ci gaba da bincike.

“Garin Jimeta ne kawai abin ya shafa, Yola da sauran wurare babu matsala,” in ji Malam Aminu.

Sai dai ya ce zuwa yanzu hankali ya kwanta kuma dokar takaita zirga-zirgar ta fara aiki, indaa aka rufe kasuwanni da sauran wurare.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here