Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kisan Abdulkarim Na-Allah, babban ɗan Sanata Bala Ibn Na’Allah, a Kaduna.
Na’Allah shi ne Sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya.
Idan za a iya tunawa, ‘yan sanda sun tabbatar da kisan Abdulkarim Na-Allah a ranar 29 ga watan Agusta, lokacin da aka tsinci gawarsa a gidansa da ke Malali GRA, Kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Laraba.
Karanta Wannan: Majalisar Dokokin Kano Ta Gayyaci Shugaban Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji Na Jihar
Jalige ya ce: “Haka ne an kama mutane biyu da ake zargi, mako guda da ya gabata a Kaduna.”
Ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin kisan.
“An gano inda motar da wadanda ake zargin suka kwace daga mamacin, amma tana cikin Jamhuriyar Nijar.
Jalige ya ce “Muna tuntubar jami’an kasa da kasa don dawo da motar zuwa Najeriya.”












































