An Kama Kwamishinan Ganduje Bisa Badaƙalar Naira Biliyan Guda

Ganduje Speaking Green 2
Ganduje Speaking Green 2

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano ta kama kwamishinan ayyuka na zamanin Gwamna Ganduje bisa zargin badaƙalar Naira biliyan guda.

Rahotanni sun ce  hukumar ta kama Injiniya Idris Wada Saleh bisa tuhumar biyan  kuɗin ga kamfanonin North Stone Construction Company Nigeria LimitedArfat Multiresources Limited da 1st Step Construction ba bisa ƙa’ida ba.

Majiyarmu ta ce an yi gaggawar sakin kuɗin a watan Afrilun bana bayan da jam’iyyar APC ta faɗi a zaɓen gwamna.

Kuma an fitar da kuɗin da sunan kwangilar gyaran tituna sai dai binciken hukumar ya nuna ko ƙasa ba a yayyafa musu ba.

Kawo yanzu dai hukumar ta fara karɓar shaida daga ma’aikatan gwamnati bisa yadda aka basu umarnin sakin kuɗin cikin gaggawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here