An gudanar da jana’izar shahararren ɗan jarida kuma masani a kafafen yada labarai, Aliyu Getso, a Kano

WhatsApp Image 2025 10 05 at 11.12.18 750x430

Daruruwan mutane daga Kano da jihohin makwabta sun halarci jana’izar tsohon ɗan jarida kuma mai fafutukar kare hakkin ma’aikata, Malam Aliyu Abubakar Getso, wanda ya rasu da safiyar Lahadi a Kano.

An gudanar da sallar jana’izarsa a unguwar Janbulo, kuda da jami’ar Bayero ta Kano, ƙarƙashin jagorancin Liman Mukhtar Shu’aibu Labaran da misalin ƙarfe 9:39 na safe.

Malam Aliyu Abubakar Getso ya rasu yana da shekaru 69, bayan ya dade yana fama da rashin lafiya.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa marigayi Getso ya taɓa zama sakatare na ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa, reshen Kano (NUJ), da kuma mataimakin sakatare na ƙungiyar ma’aikata ta ƙasa (NLC) a jihar.

Late Aliyu Abubakar Getso

A tsawon aikinsa, ya yi aiki da ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano da kuma tashoshin rediyo da dama irin su Rediyon Jihar Kano, Freedom Radio, Vision FM da Premier Radio, inda ya shahara wajen iya magana da ƙwarewa a aikin yada labarai.

Marigayin ya yi suna a Arewa saboda ƙwarewarsa wajen nazari da fassarar al’amuran cikin gida da na waje, wanda ya taimaka wajen wayar da kai da fahimtar jama’a.

Ya rasu ya bar mata uku, ‘ya’ya da jikoki.

A cikin waɗanda suka halarci jana’izarsa har da tsohon shugaban NUJ na Kano, Abbas Ibrahim, tsohon ma’aikacin BBC kuma malami a jami’ar Bayero, Dakta Maude Rabi’u Gwadabe, da manajan Dala FM, Alhaji Ahmad Garzali Yakubu, da wasu da dama.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here