An fara sanar da hukuncin zaɓen gwamnan Kaduna ta manhajar Zoom

L R Uba Sani and Isah Ashiru
L R Uba Sani and Isah Ashiru

Kotun sauraron kararrakin zaɓen gwamnan jihar Kaduna ta fara sanar da hukunci ta manhajar Zoom.

Tun farko an kafa majigi da kyamarori a kotun, inda daga bisani alƙalai suka bayyana ta manhajar Zoom, suka fara sanar da matsayar kotu.

Ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar PDP, Isa Ashiru ne ke ƙalubalantar nasarar gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC.

An tsaurara matakan tsaro a harabar kotun domin gudun tashin hankali bayan sanar da hukuncin kotun.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here